fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Majalissar dattawa na shirin tsige shugaba Buhari kan matsalar tsaro

A yau ranar laraba wasu daga cikin sanatoci suka bukaci a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda ya kasa magance matsalar tsaro a kasar.

Karamin shugaban sanatocin, Philip Aduda ne ya jagoranci sanatocin inda har ya bukaci shugaban babban shugabansu Ahmad Lawal ya waiwaye wannan lamarin.

Amma sai dai Lawal yayi watsi da wannan bukatar tasu, yayin da shi kuma karamin shugaban yace sun baiwa shugaban kasar makonni shida ya magance matsar tsaron ko su tsige shi.

A kwanakin baya shugaban kasar yace mulki akwai wahala kuma ya kosa ya sauka, wanda hakan yasa wasu manyan ‘yan kasa Najeriya kamar su Hakeem Baba Ahmad sukace kawai yayi murabus.

Leave a Reply

Your email address will not be published.