Sanata gabashin jihar Niger, Musa ya koka kan matsalar tsaron da kasar Najeriya ke fama dashi ta kashe kashe da kuma garkuwa da mutane.
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels ranar lahadi,
Inda ya bayyana masu Babagana Mungono, tsohon shugaban soji mau ritaya ya kamata yayi murabus a matsayin mai bawa hafsoshin tsaron kasar nan shawara.
Inda yace don ya gaza ba zai iya ba, saboda ‘yan ta’adda suna tura masu wasika kafin su kai hari amma rudunar sojin bata daukar mataki akan lokacin har sai sun kawo harin sun aikata bannar tasu.
Kuna a karshe yace koda ace shine akan wannan mikimin to murabusa kawai zai yi don tabbas yasan da cewa ya gaza.