A jiya ranar laraba 20 ga watan Yuli Majalissar tarayya ta nemi a kara yawan dakarun soji a jihar Taraba saboda yawan kashesu da ‘yan bindiga keyi.
Sannan kuma tace hakan zai taimaka wurin kawo karshen ta’addanci a jihar bakidaya domin ‘yan bindiga suna matukar takuta masu.
Kuma Majalissar ta nemi hukumar dake bayar da agajin gaggawa ta NEMA dama sauran hukumomi dasu cigaba da taimakawa mutanen da sukayi hijira daga yankunan su saboda matsalar tsaron.