Makafi a Jihar Sakkwato sun koka kan batun rage yawan amfani da takardun kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke shirin yi.
Sun bayyana cewa ce a duba yanayin da suke ciki na larurar gani a yawaita takardun domin su sami damar hada-hada da kudin kamar kowa tun da ba su da halin taransifa da wayoyinsu.
Yaya kuke kallon wannan koke nasu?