Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya nuna damuwa kan yanda ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a kasarnan inda ya bada shawarar da yace ita kadai ce zata kawo zaman lafiya a kasarnan.
Gwamna Tambuwal yayi wannan maganane a yayin da yake ganawa da dalibai da kuma matasa akan harkar tsaro.
Ya bayyana cewa ya kamata a majalisar tarayya da gwamnatin tarayya su saka dokar daurin rai da rai ko kuma kisa ga duk wanda aka samu da makami.
Yace yanda za’a yi abin shine a baiwa duk wani me dauke da makami damar ya je ya mai rijista idan kuma ba za’a iyawa makamin nashi rijista ba to ya mikawa gwamnatishi a mayar mada da kudinsa.
Daga nan kuma sai a saka dokar cewa duk wanda aka kama da makami to daurin rai da rai ne ko kuma kisa.
Ya kuma ce daukar karin jami’an tsaro da gyara musu Albashi da kuma sama musu yanayin aiki me kyau shima zai taimaka wajan maganin wannan matsalar.