Shugaban kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta ASUU, Emmanuel Osodoke ya bayyanawa menema labarai cewa makonni biyu sun yi yawa da shugaba Buhari ya bayar.
A yau ranar talata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministan Ilimi, Adamu Adamu cewa ya gaggauta kawo karshen hajin aikin ASUU cikin makonni biyu.
Amma shugaban malaman jami’ar ta ASUU ya bayyanwa manema labarai cewa makonni biyu yayi yawa domin ko cikin kwana daya zuwa biyu zasu iya magance matsalar
Domin yace sun kammala tattaunawa da gwamnatin abinda ya rage shine gwamnatin ta amince ta bukatunsu kawai sai su janye yajin aikin