fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Malam Abdullah Usman Gadon Kaya Yayi tir da Shigar Fitsara da Wasu ‘ya ‘yan manya ke yi, A yayin bukukuwan Auransu

Shahrararan Malamin Musulunci Malam Abdallah Usman Gadon Kaya ya magantu, inda yayi Kira da lalle ya zama wajubi Musulami su ji tsoran Allah tare da kiyaye hakkokin sa.

Malamin na wannan furucin ne, bayan wasu hotonan Bikin wasu ‘ya ‘yan manya da a kai a satin nan, wanda ya watsu a kafafan sadarwa na zamani da ya dauki hankula.

Hotunan wadanda a ka hangi Amarya ta sanya wasu kaya da su ka saba da tarbiyyar Addinin Islama gami da Al”adar mutanan Arewa.

Malamin ya bayyana hakan ne a shafin sa dake kafar sadarwa da cewa “FITO NA FITO DA ALLAH ! Baiyana Tsiraici da Fitsara! Irin Hotunan da Yaran mata na Manyan Kasar nan Suke dauka a Bikinsu sun Munana . kuma a gaban Iyayensu ! Wannan yana nuna Rashin Dattaku, da cin Zarafin Tarbiyyar Musulunci . Yaya zamu samu Albarka a kasar mu ! Allah y shrysu.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya zata dauki ma'aikata miliyan 1 su yi aikin kidaya

@abdallahgkaya

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.