fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana dalilinsa na ficewa daga APC

Sheikh Ibrahim Khalil, fittacen malamin addinin Musulunci kuma shugaban majalisar malamai a Kano ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.

Malam Ibrahim Khalil ya sanar da ficewar tasa ce daga APC a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikici tsakanin bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Shehin malamin ya shaida wa BBC cewa: “To ni a matsayina na dan jam’iyyar APC kuma daya daga cikin dattawa da kuma daya daga cikin caucus, abin da nake so in tabbatar shi ne na fita daga jam’iyyar APC.”

“Komai a rayuwa mai dalili ne. Dalilai iri uku ne: ko dai masu ilimi da hankali su sani, ko kuma kowa da kowa su sani, ko kuma mutum shi ya san dalilinsa,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko ya fice ne daga APC saboda wasu na cewa sun sauke shi daga jagorantar majalisar malaman jihar ta Kano, sai ya musanta haka.

Ya kuma ce har yanzu yana nan a matsayinsa na dan siyasa.

“Ai ban daina siyasa ba, kuma ban ce ba zan yi jam’iyya ba. Dama shiga ta ANPP ba ni na kai kaina ba, masoya ne suka yi min rajista a jam’iyyar. Don haka yanzu ne zan shiga jam’iyyar da na ga dama da kaina.”

Da aka tambaye shi ko zai fito takarar mukamin gwamnan Kano, sai ya ce, “Dama ban taba cewa na daina takara ba domin takara ta jama’a ce, kuma su suka neme ni in yi, sannan ba su ce in daina ba.”

Daga BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.