Karamin ministan Ilimi, Emeka Nwajuiba ya bayyana cewa, malamai dake yajin aiki karkashin kungiyarsu ta ASUU basu cancanci a biyasu Albashiba.
Yace sam bai dace ba ace malaman basa zuwa aiki, suna yajin aiki sannan su rika karbar albashin daga gwamnatin tarayya ba.
Yace amma matsalar itace idan aka dakatar da albashinsu shine bayan janye yajin aikin, zasu kuma zo suna neman a biyasu albashin watannin da basu yi aikin ba.
Ministan yace yajin aiki abune da aka yi amfani dashi a shekarun baya.
Yace shi kanshi yana da yara 2 dake makaranta a jami’ar gwamnati kuma yana jin ba dadi akansu da sauran yaran iyaye.