fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Malamai sun amince da dakatar da sallar Juma’a a Kano

Malamai a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun amince da dakatar da sallar juma’a a daukacin masallatan jihar, a yayin da dokar hana fita da gwamnati ta saka ke fara aiki a yau Alhamis.

Malaman dai sun gudanar da taron nasu ne a Africa House da ke fadar gwamnatin Kano ranar Alhamis, karkashin kwamitin kar ta kwana na cutar korona da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa.

Idan an jima ne dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa za ta fara aiki, wadda za a shafe tsawon mako guda.

Shawararin malaman dai na zuwa ne bayan da hukumomi a jihar Kano suka sanar da mutuwar wani mutum mai dauke da cutar korona a jihar, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum 21.

Wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ce Malaman sun yi nazarin harkokin rayuwar al’umma ne wadanda ke da nasaba da taron jama’a da nufin bayar da fatawa, inda suka amince da dakatar da Sallar Juma’a a masallatan jihar da kuma tarukan da ake yi da suka shafi karatu a lokacin watan Ramadan, don hana yaduwar cutar korona a tsakanin al’umma.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

Dr. Ibrahim Mu’azzam mai Bushira shi ne sakataren karamin kwamitin malamai da kwamitin kar ta kwana na coronavirus ya kafa, wanda ya ce malaman sun amince da a dakatar da gabatar da Sallar Juma’a don gudun kada wani da yake dauke da cutar ya yada ta a tsakanin al’umma.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.