Wani malamin addinin gargajiya Nurudeen Oyero ya bayyana cewa yana goyon bayan Tinubu dari bisa dari a zabe mai zuwa.
Ya bayyana cewa shi da gabadaya mabiyanshi zasu marawa dan takarar shugaban kasar na APC baya domin su tabbatar da cewa yayi nasarar lashe zaben.
Malam ya kasance shugaban malaman Ifa na jihar Legas, kuma yayi wannan bayanin ne a jihar a wani taron da suka gudanar.