Tsohon dan majalisar Dattijai da ya Wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijai, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, Malaman Kiristoci na ta magana akan matsalar kashe-kashe dake faruwa.
Yace amma a bangare daya kuma, Malaman Addonin Musulunci sun yi shiru dan kada su batawa Gwamnati rai.
Ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta.
Koda a kwanakinnan, babban limamin coci a Sokoto, Bishop Kuka ya bayyana cewa, ana wa kiristoci kisan kiyayya wanda gwamnati ta mayar masa da martanin cewa ba gaskiya bane.