Wani babban malamin jami’ar jihar Ogun ta UNN, Dr. Michael Ugwueze dake koyar da lilin siyasa ya cewa dalibansa yin katin zabe shine C.A test din sa.
Malamin ya bayyana cewa ya masu hakan ne domin su san ‘yancin su da kuma hakkokin kasa suka wajabta akansu, kuma maki talatatin ne Test din nasa.
Ya kara da cewa wani abinda ke bashi mamaki shi yawanci yana tambayar daliban shekarar karshe a jami’ar cewa sun taba yin zabe, amma sai suce masa a’a wasu basu da katin don suna jin cewa wanda suka zaba ba shine ake ba mulki ba.