Wani malamin makarantar sakandiri ta Simple Faith dake jihar Legas, Steven ya zane dalibinsa dan JS 2 Emmanuel Amidu wanda hakan yasa ya fara amai har ya mutu.
Mahaifin yaron Akinola Amidu ya bayyana cewa a makaranta ne aka zane shi saboda bai kammala Home-Work dinsa ba.
Kuma sunyi kokarin kaishi asibin Legas dake Surulere wanda a can ne ya mutu. Mahaifin nasa yayi kira ga gwamnati da hukumar ‘yan sansda cewa su kama wannan malamin a hukunta shi kan abinda ya aikata.