fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Mamayarmu sukayi bamu san zasu kawo mana harin ba, shugaban jami’an gidan Yari na Kuje

Gidan Yarin Kuje da ‘yan bindiga suka kaiwa harin sun bayyana cewa mamayarsu suka yi domin basu da masaniya akan harin.

A ranar talata da daddare na ‘yan bindigar suka kai hari gidan yarin dakw Abuja inda suka bude masu wuta tun karfi goma na dare har zuwa daya kafin suka tsere.

‘Yan ta’addan ISWAP suka kai wannan mummunan harin kuma sun saki mutane da dama sun tsere a gidan yarin hadda ‘yan Boko Haram.

Mai magana da yawun jami’an gidan yarin na Kuje, Umar Abubakar ya bayyanawa manema labarai cewa mamayrsu suka yi basu san cewa zasu kawo masu harin ba.

Karanta wannan  Rundunar sojin Najeriya ta damke wani kasurgumin dan ta'addan ISWAP daya tsere a gidan kurkukun Kuje

Kuma yace sun kashe masu jami’i daya sannan mutane da dama sun tsere daga gidan gyara halin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.