fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Man United zasu iya rasa Jadon Sancho saboda dalili guda daya

Manchester United suna harin siyan Jadon Sancho daga kungiyar Dortmund a wannan kakar wasan bayan Ole Gunnar yayi kokarin siyan shi a kakar wasan bara. Kuma United sunyi kokarin siyan Sancho tun 2017 a lokacin daya koma Dortmund.

Yanzu kuma manema labarai na ESPN sun bayyana cewa kungiyar Bayern Munich sun shiga gasar siyan Sancho daga kungiyar Dortmund duk da cewa su abokan hamayya ne, sai dai an samu labari cewa Munich zasu siya Sancho idan suka rasa tauraron  City Sane.
Jadon Sancho yana kokari sosai a wannan kakar wasan yayin da yayi nasarar jefa kwallaye har guda 14 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 15.
Dortmund sun sakawa Sancho farashin euros miliyan 100 kuma basu da burin rage komai akan hakan musamman ma idan abokan hamayyar su ne zasu siye shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *