Sojojin Najariya sun bayyana cewa, rahoton dake nuna cewa basu da isassun kayan aiki karyace.
Hukumar sojan ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace maganar rashin kula da hakkokin sojojin da kuma saka bangaranci da addini a harkar soja ba gaskiya bane.
Tace tana kira ga sojoji da su dukufa wajan gudanar da ayyukansu.
Troops deployed in ongoing operational engagements are putting in their best for the nation & should be encouraged, rather than plotting disaffection amongst them. https://t.co/lSN4B8M8jS
— Nigerian Army (@HQNigerianArmy) June 29, 2022
Hukumar tace kamata yayi a rika karfafawa kokarin da suke na kawo zaman lafiya ba kashe musu karfin gwiwa ba.