fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Manajan Chelsea Frank Lampard ya zabi gwanin shi tsakanin Messi da Ronaldo

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun kasance manyan abokan takara a duniyar wasan kwallon kafa fiye da shekaru goma da suka gabata yayin da kuma suka sunayen su suka shiga cikin jerin zakarun yan wasan kwallon kafa na duniya bakidaya.

Lionel Messi ya buga gabaya wasannin shi a kungiyar Barcelona wadda yayi kusan shekaru 20 a kungiyar kuma yayi nasarar cin kwallaye 636 a wasanni 737 daya buga. Messi ya lashe kofunan La Liga sau goma a Barcelona tare da kofunan gasar zakarun nahiyar turai guda hudu.
Shi kuma Cristiano Ronaldo ya buga wasannin shine a kungiyar Sporting CP, Manchester United, Real Madrid da kungiyar shi ta yanzu wato Juventus. Cristiano yayi nasarar cin kwallaye 641 a wasanni 852 yayin da kuma ya lashe kofunan mayan gasa na wasan kwallon kafa a kasashe guda uku tare da kofunan gasar zakarun nahiyar turai guda biyar sai kofin gasar kasashen nahiyar turai wanda ya lashe da kasar shi ta Portugal.
Manajan Chelsea Frank Lampard ya zabi gwanin shi tsakanin Messi da Ronaldo inda yake cewa “Messi ne gwarzon yan wasan kwallon kafa saboda shi dan baiwa ne kuma shima Cristiano Ronaldo yayi abin burgewa sosai”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Shalelen PSG, Mbappe ya samu sabani da Messi kan sayar da Neymar a wannan kakar

Leave a Reply

Your email address will not be published.