fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Manajan Chelsea ya kalubalanci tsarin buga wasannin gasar Premier League

Kungiyar Chelsea, wadda ta kasance ta biyar a saman teburin gasar Premier League zata kara da Arsenal ranar sati sannan kuma zata karbi bakunci  Aston Villa ranar litinin, wanda hakan yasa manajan kungiyar Lampard ya kalubalanci tsarin buga wasannin saboda ya banbanta dana sauran kungiyoyi.

Tsarin wasannin ya nuna cewa awanni 48 ne tsakanin wasannin Chelsea guda biyu kuma Lampard ya bayyana cewa yan wasa suna cikin hadari idan har suka saki jiki suka jajirce sosai a gabadaya wasannin.

A karshe Lampard yace suna bukatar lashe gabadaya makin wasannin kuma akwai wasu kungiyoyin da suke fafatawa a saman teburin gasar wanda su suke da hutun kwanaki uku zuwa hudu tsakanin wasannin nasu kamar su Manchester United,Tottenham da kuma Liverpool.

Leave a Reply

Your email address will not be published.