fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Manchester United 0-0 Chelsea: Yayin da Edinson Cavani ya fara buga wasan shi na farko a kungiyar Manchester

Sabon dan wasan Manchester United wanda ta siya a ranar da aka kulle kasuwar yan wasa, Edinson Cavani ya fara bugawa kungiyar wasa a yau bayan tayi mai mai canji a minti na 58 a wasan da suka tashi 0-0 tsakanin su da Chelsea a gasar Premier league.

Manchester United ta cigaba da rashin nasara a wasannin ta na gida har guda uku data fara bugawa na wannan kakar wanda hakan ya kasance karo na farko tun kakar 1972/73. Kocin Chelsea Lampard ya yabi golan shi Mendy bayan an tashi saboda kwallayen daya yi nasarar cirewa a wasan.
Kiris ya rage kungiyar Chelsea ta samu penariti bayan Harry Maguire ya bugi Azplicueta amma alkalin wasan bai bayar da penaritin ba wanda hakan yasa kaftin din Chelsea ya kalubalanci na’urara VAR a bayanan daya yi bayan an tashi wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kungiyar PSG ta kori kocinta Maurizio Pochettino

Leave a Reply

Your email address will not be published.