Manchester United ta fara jagorantar wasan cikin minti biyu bayan Bruno Fernandez yayi nasarar zira penariti amma Tanguay Dembele da kuma Heung Min Son suka zira kwallaye wanda suka sa Tottenham ta fara jagorantar wasan a minti na 7.
Antony Martial ya samu jan kati a minti na 28 bayan ya bugi Erik Lamela yayin da kuma kane ya zira kwallon shi ta farko a wasan shi kuma Son ya ci ta biyu wadda hakan yasa aka ci United kwallaye hudu tun kafin aje hutun rabin lokaci karo na farko a tarihi.
Serge Aurier yayi nasarar ciwa Spurs kwallo ta biyar a wasan kafin Harry Kane ya zira kwallon shi ta biyu wadda tasa Mourinho ya lallasa tshohuwar kungiyar tashi 6-1 bayan ya ziyarce ta yau a filin Old Trafford.
Wannan shine karo na uku a tarihi da aka ci Manchester United kwallaye shida a wasa guda.