Kocin manchester United na wucin gadi, Ralf Rangnick ya bayyana cewa kungiyar ba zata cancanci buga gasar zakarun nahiyar turai ba idan har suka cigaba da wasa kamar yadda suka ui jiya a hannun Everton.
Kocin jamus din ya fara horas da United ne biyo bayan korar Ole Gunnar da suka yi a watan nuwamban daya gabata, amma wasanni takwas kacal yaci cikin 17 da suka gabata.
Kuma kocin ya kara da cewa abin kunya ne ace Manchester ta kasa zira ko kwallo guda a ragar Everton, bayan ko Burnley ta zira mata kwallaye uku a wasan da suka buga.