fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Manchester United bata da sauran damar siyan Jadon Sancho>>Dortmund

Manchester United ta rasa damar siyan tauraron dan wasan da take hari a wannan kakar Jadon Sancho, yayin da har Dortmund ta samata wa’adin siyan dan wasan 10 ga watan augusta amma ta tsallake wannan wa’adin.

Borussia Dortmund tayi burus da tayin da Manchester ta yiwa dan wasan na yuro miliyan 91.3 a cikin wannan makon kuma yanzu darektan wasannin kungiyar Zorc ya bayyana cewa United bata da sauran damar siyan dan wasan a wannan kakar.

Hatta shugaban kungiyar Lucien Favre da yan wasa da sauran ma’aikata tare da masoyan Dortmund basa son siyar da Jadon Sancho a wannan kakar. Kaftin din kungiyar Marco Reus shima ya bayyana cewa Sancho zai kara shekara guda a kungiyar.

Kungiyar bata ba sauran yan wasan ta damar tattaunawa da manema labarai akan lamarin Sancho ba amma duk da haka sai da Thomas Meuiner ya bayyanawa Sky Sport cewa Sancho ba zai bar kungiyar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.