Manajan Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana cewa tauraron dan wasan shi Edinson Cavani zai taka muhimmyar rawa a kungiyar yayin da kuma ya kara da cewa dan wasan zai iya sabunta kwantirakin shi a kungiyar.
Edinson Cavani ya koma kungiyar Manchester United ne daga Paris Saint German a kyauta da kwantirakin shekara daya tare da zabin karin watanni 12, bayan ya bar kungiyar PSG wadda ya dauki tsawon shekaru 7 yana buga mata wasa.
Wasa daya kacal Cavani ya fara bugawa Manchester daga farko, yayin da kuma yayi nasarar cin kwallaye 3 a wasanni takwas daya buga mata amma saidai yawancin wasannin nashi daga benci yake shigowa yayin da har ya taimakawa Fernandez yaci kwallo guda a wasan su da Leicester City.