fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Manchester United ta nada kocin Ajax Erik Ten Hag matsayin sabon kocinta

Dan kasar Netherlands, mai shekara 52, zai karbi aiki daga wurin kocin rikon-kwarya Ralf Rangnick a karshen kakar wasa a kwantaragin shekara uku, amma yana da zabin tsawaita kwangilarsa da shekara daya.

Manchester United ta ce nadin nasa ya ta’allaka ne da samun bizar aiki a Ingila.

Rangnick, wanda ya zama kocin kungiyar bayan ta kori Ole Gunnar Solskjaer a watan Nuwamba, zai koma matsayin mai bayar da shawara a kungiyar.

“Babban abin alfahari ne da aka nada ni a matsayin kocin Manchester United kuma na yi matukar shiryawa don tunkarar kalubalen da ke gabana,” in ji Ten Hag.

“Na san tarihin wannan babbar kungiyar da kuma kaunar da magoya bayanta suke mata, kuma zan zage dantse wajen samar da tawaga wacce za ta yi nasara.”

Ten Hag zai zama kocin United na biyar tun bayan ritayar Sir Alex Ferguson a 2013.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *