Kungiyar Manchester United ta sha kashi daci biyu da daya a hannun Brighton a wasanta na farkon kakar bana wanda sabon kocinta Ten Hag ya fara jagoranta.
United bata fara buga wasan da zakaran gwajinta Ronaldo ba, wanda hakan yasa masoyan kungiyar ke caccakar kocin kan wannan ra’ayin nasa.
Amma ya kare kansa tun kafin a fara wasan inda yace Ronaldo bai yi atisayi sosai ba sai yasa bai fara buga wasan dashi ba.
Grob ne ya ciwa Brighton kwallaye biyu a wasan yayin da Allister yayi kuskuren cin gida wanda hakan yasa aka tashi daci 2-1.