Dan Kwallon kafar kasar Senegal me bugawa kungiyar Liverpool wasa, Sadio Mane ya taimakawa kasarsa da kwallo wadda suka samu nasara akan Guinea Bissau da 2-0.
Da wannan nasara, Senegal ta samu kaiwa ga buga gasar Cin kofin Nahiyar Africa a 2022.
A mintuna 82 ne Mane ya saka kwallon data basu nasara wanda a yanzu suna da maki 12 kenan.