fbpx
Monday, December 5
Shadow

Mansurah Isah ta daina bibiyar wata mawakiyar kasar Amurka saboda fitsararta tayi yawa

Tsohuwar tauraruwar finafinan Hausa kuma mata a gurin Dani Musa Danja watau Mansurah Isah ta bayyana cewa ta daina bibiyar shahararriyar, fitsararriyar mawakiyar kasar amurkarnan watau Nicki Minaj saboda wasu hotunan fitsara wanda take kusan tsirara da mawakiyar ta wallafa a wata mujallar kasar Amurka.

Hotunan mawakiyar dai da take da miliyoyin mabiya sun watsu sosai tun bayan data wallafasu kamar yanda hakane dama burinta. Mansurah Isah tace duk da tasan cewa mawakiyar bata damu ba dan ta daina bibiyarta amma zata yi hakan, ta kara da cewa a baya tana ta kauda kai ga irin kurakuran da mawakiyar ta rika yi amma wannan watsa hotunan tsirara kam yayi yawa.

Haka kuma Mansurah ta kara da cewa irin su Nicki Minaj ne suke sa mutane killace ‘ya’yansu daga shiga yanar gizo kuma ba zasu taba amincewa da ‘yna cin yara na shiga yanar gizo yanda suka ga dama ba.

Karanta wannan  Kwanaki 3 da bude gidauniyar tallafawa Tinubu, har an tara masa Naira Miliyan 24

Ba wai Mansurar bace kawai tayi Allah wadai da wadannan hotunan na Nicki ba Harma wata abokiyar aikin ta wadda take waka  irin tata a kasar ta Amurka tace abinda Nickin tayi bai dace ba, ita a ganinta lokaci ya wuce da Nickin zata rika irin wannan shashancin lura da cewa akwai ‘yan mata da dama dake kallonta a matsayin abar koyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *