Duk da cewa ya ajiye mukaminsa saboda rashin lafiya, Amma majalisar Tarayya tace dole a hukunta tsohon alkalin Alkalan Najariya, Justice Ibrahim Tanko Muhammad.
Majalisar ta dauki wannan matsayane a zaman da ta yi inda tace dole a tsaftace bangaren shari’a.
Saidai ta nemi a kara kulawar da akewa alkalan dan kawar da kansu daga aikata ba daidai ba.
Alkalai 14 ne dai na kotun kolin ke zargin Justice Ibrahim Tanko Muhammad da rashawa da cin hanci.
Wasu daga cikin laifukan da suke zarginshi akai sun hada da:
Rashin biyansu hakkokinsu.
Rashin canja motocin da suka lalace.
Matsalar wajan zama.
Rashin magani a asibitin kotun.
Rashin tsayayyar wutar lantarki.
Rashin Internet.
Da dai sauransu.
Saidai Justice Ibrahim Tanko Muhammad duk ya karyata wadannan zarge-zarge da ake masa.