fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Manyan Mutanen Arewa sun goyi bayan maganar Gwamna El-Rufai na cewa a barwa kudu shugaban kasa a 2023

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi kiran cewa a barwa ‘yan kudu shugaban kasa a shekarar 2023 inda yace bayan shugaba Buhati ya kammala shugabancinsa dan kudune ya kamata mutanen Arewa su goyawa baya.

 

Wannan ra’ayi nashi ya zo daidai dana wasu manyan Arewa, cikinsu akwai Tanko Yakasai wanda hadimin tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari ne. Hutudole ya samo muku a hirar da yayi da Vanguard cewa, idan akwai tsarin karba-karba a kundin APC ya kamata su girmama hakan inda yace shekarar 2019 da shugaba Buhati yayi takara babu wanda ya nemi kujerar shugaban kasar dan haka kudu ya kamata su barwa a 2023.

Shima Tsohon Ministan Tama da karafa, Wantaregh Paul Unongi ya bada shawarar a barwa kudu takarar shugabancin kasa a shekarar 2023. Shima dai tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Balarabe Musa ya bayyana cewa, tsarin na karba-karba yayi daidai da dokar raba daidan mukami ta kasa. Shima dai babban dan jam’iyyar PDP, Idris Bello Dambazau ya bayyana cewa yana goyon bayan ra’ayi  na El-Rufai.

Karanta wannan  Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Rivers ya tsallakw rijiya da baya yayin da 'yan bindiga suka kashe masa jami'in dake tsaron sa

 

Sauran sune, Dr. Saidu Ahmad Dukawa na jami’ar Bayero dake Kano da Dr. Yunusa Tanko wanda shine kakakin kungiyar ceto Najeriya ta NCFront,  dadai sauransu.

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.