fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Maryam ta musanta cewa ita ta kashe mijinta: ‘Yan uwanta na taimakamata wajan canja labarin

Labarin Bilya dan gidan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Bello Halliru da matarshi Maryam ta kaseshi sanadiyyar kishi bayan ta ga wani sakon waya a wayarshi, ya dauki sabon salo, Mutane sunyi ta kiran cewa ya kamata a hukunta Maryam dan ya zama wa’azi ga duk wata da take da niyyar yin hakan.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A wani labari da abokin mamacin ya wallafa kuma yake ta watsuwa a dandalin sadaa zumunta, ya bayar da labarin ainihin yanda lamarin ya faru da kuma yanda kisan Bilya ya kasance, bayan da taga wasikar Maryam tace Bilya ya saketa ko kuma ta yankemai mazakutarshi.
Shi kuma sai be biyemataba, abokinshi yazo aka kira wani daga cikin danginta da danginshi Bilya din suka sasantasu suka basu hakuri, kamar ta hakura, a hakan ta dauko kwalba ta fasa ta nufo kan Bilya da ita ya kamata ya kwace, garin haka har yaji ciwo ta cijeshi a hannu.
Daga karshe dai abu ya lafa kamar komi ya wuce dare yayi kowa ya watse aka barsu daga shi sai ita, cikin dare ta dauko wuka yana bacci ta caccaka mai kuma tayi kokarin cika alkawarin da tayi na yankemai maza kita amma ta kasa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Daga baya da kanta ta kaishi asibiti kamar yanda labarin ya bayyana, kuma a asibitin likita yayi kokarin shawo kanta ta gayamai itace ta kashe mijin nata.
Aka kira ‘yan sanda suka tafi da ita, amma da akaje gurin ‘yan sanda sai Maryam ta canja labari tace ba ita ta kashe mijin nataba, wai suna fadane yayi tuntube da kwalbar shisha ya fadi yaji ciwo datukunyar ajiye fulawa.
‘Yan sanda sunje gidan suka iske an goge duk wani jini da wata alamar abinda ya faru, kuma an batar da wukar da tayi kisan da ita an fasa kwalbar shisha da tukunyar ajiye fulawa wadda Maryam tace itace ta jima mijin nata ciwo.
Me bayar da labarin yace abin mamaki babi wata alamar nadama tattare da Maryam kuma koda irin ta nuna saduda ga ‘yan uwan mijin nata batayi ba,ya kara da cewa kawai saidai yace Allah ya biyawa Bilya hakkinshi a Lahira.
Hmmmm Duniya kenan, idan me karatu be mantaba Maryam Diyace gurin tsohuwar shugabar Kamfanin Aso, me bayar da lamuni da kuma ajiyar kudin mutane da ginawa mutane gidaje su rika biya a hankali, wadda ake kira da Maimuna Aliyu, watau dai itama kisace.
Kuma me bayar da labarin yace dan uwan Maryam dinne yaje gidanta ya kawar da dukkan wata shaida da zata nuna cewa Maryace tayi kisan,  ya dauke wukar aka batar da ita sannan aka fashe kwalbar shisha da tukunyar ajiye fulawa wadada Maryam din taci da itace mijinta yaji ciwukan jikinshi.

Karanta wannan  Fasto Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Da ‘Yan Tawayen IPOB Suka Yi Wa Fatima Da ‘Ya’yanta Hudu A Jihar Anambara

Watau idan mutum ya kalli wannan labari zai fahimci wasu abubuwa kuma zaiyi tambayoyi akan wasu abubuwa,

Maryam kodai tana da tabin hankali ko kuma tana shaye-shaye.

Me yakai kwalbar shisha gidan aure?, duk da suna cewa wai ba kwayabace,

An nunawa Maryam gata da yawa, babu wanda keso naahi ya tozarta amma akwai irin mummunan laifin da idan naka ya aikata dole kabar doka tayi aikinta, idan mutum yayi kisa kai koma ba kisaba koda ace wani savon Allahne wanda baikai kisaba kayi a karin farko to dole sai kaga mutum ya fita hayyacinshi, amma wai ace maryam bata nuna alamar sadudaba, har ta na da kwarin zuciyar da zata canja wannan labarin, tana mace?

To Allah shi kyauta, ya kuma shiryemu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.