fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Masallatai na bin dokokin Coronavirus/COVID-19 sau da kafa>>Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta tabbatarwa da gwamnatin tarayya

Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya, NSCIA da kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN sun bayar da tabbacin cewa Musulmai da Kiristoci na bin dokokin da gwamnati ta zayyana na dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 a Coci-coci da Masallatai.

 

Hakan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta koka kan cewa wasu guraren ibadar sun fatali da dokokin da gwamnati ta saka na hana yaduwar cutar.

Me magana da yawun majalisar koli ta addinin Musulunci,  NSCIA, Aselemi Ibrahim ya bayyana cewa, basu ji dadin wannan magana ta gwamnati ba domin a farko sunce kowa yayi Sallah a gida amma daga baya sai suka bada shawarar duk masallacin da zai bude ya tabbatar cewa an tanadi kiyaye  dokokin hana yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Shima sakataren CAN, Joseph Daramola ya bayyana cewa ba’a musu adalci ba idan akace wai basu bin dokokin gwamnati. Yace ba lallai bane ace suna bin kowace doka ko kuma kowace coci na bin dokokin amma kamata yayi a jinjinawa wanda suka bu dokar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *