Masana kiwon lafiya sun gargadi yan Najeriya masu shan fitsari cewa su kauracewa hakan domin yana kawo cututtuka daban daban.
Inda Dr. Olaposi ya bayyana cewa fitsari yana dauke da wasu kwayoyin cututtuka saboda mutun yana fitar da duk wasu abubuwan da basu da amfani ne a jikinsa ta hanyar fitsari.
A karshe dai ya kara da cewa fitsarin na jawo cutar kwalara, amai da gudawa, zazzabi da dai sauran miyagun cututtuka.