Za’a karrama Tauraron fina-finan Hausa Ali Nuhu (Sarki) a masana’antar fim ta kudancin kasarnan, taron karrama jaruman da ake shiryawa duk shekara da akawa lakabi da BON a takaice, zai baiwa Ali Nuhun kyautar karramawa ta jarumi na musamman.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Za’a yi wannan taronne ranar 16 ga watan Disamba idan Allah ya kaimu.
Masu bayar da kyautar sun bayyana Ali Nuhu a matsayin jiko kuma abin koyi ga matasa da yawa a Arewa da suke da burin shiga masana’antar ta finafinan kudancin kasarnan, dan hakane za’a bashi kyautar.
Muna tayashi murna.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});