fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Masoyan Barca na cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, bayan sabondan wasanta ya taimakawa kungiyar ta doke Madrid daci daya

Kungiyar Barcelona tayi murna bayan tayi nasarar doke babbar kungiyar hamayyarta wato Real Madrid a wasan sada zumuntar da suka buga a Las Vegas.

Sabon dan wasan kungiyar wanda ta sayo daga Leeds United a farashin yuro miliyan 60, Rafinha ne yayi nasarar ci mata kwallon a minti na 27.

Kuma kiris ya rage Madrid taci kwallo a wasan a minti na 17 bayan Federico Valverde ya bugo wata kwallo nesa, amma sandar raga ta cire kwallon.

Yayin aka tashi Barca na cin zakarun nahiyar turan 1-0 kuma masoyangmta sukace kwalliya ta biya kudin sabolu, saboda sabon dan wasan nata ne yayi nasarar cin kwallon.

Leave a Reply

Your email address will not be published.