fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Masoyan kungiyar Dortmund zasu iya taimakawa wajen cigaba da buga wasannin gasar Bundesliga

A ranar laraba shugaban yan sandan Dortmund Grego Lange ya bukaci masoyan wasan kwallon kafa na kasar jamus da su bayyana cewa cigaba da buga wasannin gasar Bundlesliga a wannan karshen makon ba kuskure bane, bayan cutar Covid-19 tasa an dakatar da wasannin har na tsawon watanni biyu.

Ana ta yin maganganu akan cewa watakila masoyan wasan kwallon kafa zasu taru a filin wasan Dortmund a ranar sati idan zasu buga wasa tsakanin su da kungiyar Schalke ba tare da yan kallo ba, yayin da suke shirin cigaba da wasannin nasu a karshen wannan makon.
Darektan kungiyar Dortmund Christian Hockenjos ya tabbatar da cewa zasu kiyaye dukkan wata matsala, kuma abokan aikin shi masu lura da masoyan su sun gaya mai cewa kungiyar masoyan su sun ce baza su zo filin wasan ba.
Za’a cigaba da buga wasannin gasar Bundlesliga 1 da 2 duk da cewa an samu wasu yan wasan gasar dauke da cutar Covid-19 tun da aka cigaba da atisayi a watan daya gabata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Leave a Reply

Your email address will not be published.