Lamarin ya farune akan titin Tsafe zuwa Gusau da yammacin jiya, Laraba da misalin karfe 6 na yamma.
Motoci 4 ne suka hade a hadarin. Kakakin jam’iyyar PDP a jihar, Alhaji Faruku Shattima ya tabbatarwa Punch haka. Yace mutanen suna kan hanyar tarbar gwamnan jihar, Bello Matawalle ne da ya dawo daga Abuja bayan ziyarar aikin da ya kai.
Yace sun yi taho mu gama da wata motar Dangote inda nan take su duka suka mutu. Hutudole ya fahimci an yi jana’izar marigayan da misalin karfe 10 na safiyar yau, Alhamis, Kamar yanda Addinin Musulunci ya tanada.