fbpx
Sunday, December 4
Shadow

“Masoyana kuyi hakuri da abinda zan fada, an kurenine, idan banyi magana ba to hawan jini zai kamani”>>Adam A. Zango ya caccaki masu yunkurin bata mishi suna

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya caccaki wasu wadanda yace suna batamai suna, adamun ya bayyana cewa a baya ya taimakawa mutanen amma yanzu sun koma gefe suna kokarin su bata mai suna saboda  haka sun kaishi bango kuma yana da iyali dolene ya tashi tsaye  ya kare mutuncin kanshi.

Adamun dai ya bayyana cewa shi ba dan daudu bane kuma baya maula, sannan ya bayyana cewa an mai kazafi da yawa yayi shiru, to wannan karin bazai yi shiru ba, duk da be kira sunaba amma nan gaba idan aka sake yunkurin bata mishi suna to sai ya tonawa mutum asiri.

Adamun dai ya bayyana cewa wasune sukasha alwashin sai sun ga bayanshi.

Gadai kalaman daya rubuta kamar haka:

“Ni ba dan daudu bane kuma ni ba dan maula bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi. Da ALLAH kadai na dogara. Idan kuma akwai malamin da yace na taba zuwa wajansa ko kuma wanda ya taba bani kudi kyauta ba tare da nayi masa aikin komai ba, toh dan girman ALLAH kada ya rufa min asiri tun daga kan yan siyasa, sarakuna, gwamnati, ko masu kudi, ko yammata…. duk abinda dana mallaka a rayuwata gumi na ne ya bani ba dan adam ba…motar hawa, gida ko fili…. Don haka babu wanda ya isa ya sani inyi abinda banyi niyya ba tunda babu wanda ya tayani kare mutuncin daukakata.

Karanta wannan  Anya kuwa da gaske gwamnati tana so ta kasheni>>Bello Turji

DON HAKA TA HANYA DAYA KADAI ZAKU IYA DAKATAR DA DAUKAKATA……HANYAR ITACE KU DAKATAR DA NUMFASHINA, SAI DAI KUMA KASH HAKAN BA’A HANNUNKU YAKE….HABA KUYI TA YAWO DANI KUNA BATA MIN SUNA DON KAWAI ALLAH YA FIFITANI AKANKU.
Kunce min arne kunce min gay kunce min fasiki kunce min mai girman kai amma duk da haka masoyana basu gujeni ba basu daina sayan fina finai da wakokina ba. Haba don ALLAH mai nayi muku duk wanda na taimaka a rayuwata sai ya dawo yana yakata!! Toh na kai bango……billahillazi la’ila ha illahuwa duk wanda ya kara kara tabani saina tona masa asiri. Sannan duk wanda ya rufa min asiri akan abubuwan dana lissafa ALLAH ya tona masa nasa.

Ban kira sunan kowa ba a yanzu amma next time zan kira sunan ko waye idan ya kara bata min suna ….ina da ýaýa ya zama dole in fara kare martaba na kafin yayi affecting dinsu don ALLAH kadai ya san gawar fari….sannan zanja tunga da mabiyana na kannywood…. don a haka ne kadai za’a bam bance tsakanin aya da tsakuwa…. MASOYANA KU GAFARCE AKAN ABUBUWAN DANA RUBUTA, AN KURENI NE IDAN KUMA BANYI MAGANA BA WLH HAWAN JINI ZAI IYA KAMANI.”

Allah shi kyauta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *