Wani masoyin kungiyar Arsenal yayi wata gagarumar magana akan Messi wada yaci kwallaye 30 a gabadaya wasannin daya buga a kakar wasan bara, yayin da yake cewa Lionel Messi ba zai iya cin kwallaye 20 ba a kakar wasa guda na premier league ba.
Kuma shima masoyin Barcelona ya hanzarta wurin mayar da martani akan wannan maganar, yayin daya saka wani bideyo a kafar sada zumuntar ta Twitter wanda Messi yake lallasar Arsenal a shekara ta 2010. Kuma bayan wannan bideyon sai yace Messi yaci Arsenal kwallaye 4 cikin mintina 90 saboda haka ya kamata kaji kunya.

Tun daga nan kuma masoyan wasan kwallon kafa suke ta yin musu a kafar sada zumuntar akan wannan maganar ta cewa Messi ba zai iya cin kwallaye 20 a kakar wasan premier league guda ba. Yayin da wani yake cewa Messi zai ci kwallaye 20 a wasanni biyar da babbar tawagar da Arsenal suke ji ita a tarihi.