fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Masu A daidaita Sahu Sun Fara Yajin Aiki a Jihar Kano

Fasinjoji a cikin garin na kano sun kasance cikin rudani biyo bayan fara yajin aikin na sai baba-ta-gani da masu kekenapep suka fara, wanda akasari ake kira Adaidaita Sahu, a jihar a ranar Litinin.

Sun shiga yajin aikin ne don kin biyan harajin N100 da gwamnatin jihar ta sanya ta hanyar Hukumar Kula da Hanyoyi da Motoci ta Jihar Kano (KAROTA) da sauran batutuwa.
Sun ce matakin ya zama dole don kauce wa abin da suka bayyana da kwace da sunan haraji da sauran tarar.
Yawancin tituna a cikin birni sun kasance ba kowa sai dai motoci masu zaman kansu, motocin safa, motocin haya, babura, da manyan motoci ke bin hanyoyin.
Aminiya ta ruwaito cewa mafi yawan matafiya masu matsakaicin matsayi da ke zuwa wuraren ayyukansu da kuma daliban da ke zuwa makaranta sun koma yin tattaki don isa inda suke.
Wannan shi ne sakamakon rashin yin jigilar jama’a a cikin jihar.
Gwamnatin Jihar, a ranar Lahadin da ta gabata, ta gabatar da tsare-tsare ga wani kamfanin sufuri don samar da motocin bas 200 kafin karshen 2021.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *