A ranar Laraba ne Cibiyar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Afrika CDC ta bayyana cewa, a halinn yanzu akwai masu fama da cutar korona 612,586 a nahiyar Afrika.
Cibiyar ta bayana haka ne a sakon da ta wallafa a shafin ta na tiwita ranar Laraba in da ta ce, yawan masu cutar ya tashi daga 594,841 a ranar Talata zuwa 612,586 a ranar Laraba da safe.

Cibiyar ta kuma bayyana cewa, cutar ta kashe mutum 13,519 a kididdigar da aka yi a wannan lokacin.
An kuma samu nasara wakewar mutum 307,069 da suka kamu da cutar tunda farko.
Bayani ya kuma nuna cewa, kasar Afrika ta Kudu ce cutar ta fi addaba daga nan kuma sai kasashen Egypt, Nigeria, Ghana, Algeria, Morocco, da kuma kasar Cameroon.
Kidididgar ta kuma nuna cewa, yankin Afrika ta Yamma ce ya fi fama da cutar daga nan kuma sai kuma yankin gabashi da tsakiyar yankin Afrika.