fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Masu fasa kwauri sun kaiwa jami’an kwastam hari suka kwace makamansu da kuma trelar shinkafa

Wasu da ake zargin masu fasa kwauri ne a jihar Legas sun afkawa jami’an kwastam inda suka kwace musu makamai da wata mota cike da shinkafa.

 

Lamarin ya farune a yankin Oke-Odo na jihar.

 

Maharan sun je da yawa inda suka sha karfin jami’an kwastam din yayin da suke kan hanyar kai shinkafar da suka kwace ofishinsu.

 

An jikkata jami’in kwastam daya da kuma tafiya da Bindigarsa.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna kan bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published.