Masu garkuwa da mutane a jihar Taraba sun ki sakin wata mata mai juna biyu da ta yi fama da nakuda a hannunsu tare da neman ‘yan uwanta da su biya ta kudin fansa.
An tattaro cewa ‘yan bindigar sun sace matar mai dauke da juna biyu ‘yar watanni 9 da kuma wasu mutane shida ciki har da Sharabilu Maaji Bala daya, a Jalingo.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, masu garkuwa da mutanen sun dira a Unguwar Primary Board da ke Jalingo da karfe 3 na safiyar ranar Asabar 16 ga watan Afrilu, inda suka yi awon gaba da mutanen.
Sai dai masu garkuwa da mutanen sun kira mahaifin matar mai ciki da aka sace, inda suka bukaci a biya su kudin fansa cikin gaggauwa, inda suka ce matar tana fama da naƙuda.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da sace matar mai juna biyu da wasu mutane shida amma bai bayar da cikakken bayani ba.