Masu garkuwa da mutane a Kaduna sun kashe soja me mukamin Kanal da suka kama a kwanakin baya duk da biyansu kudin fansa na Miliyan 10.
Yan bindigar sun kama SB Onifade a kusa da kamfanin Olam dake Kaduna ranar 27 ga watan Satumba inda kuma suka nemi kudin Fansa.
Wata majiya ta gayawa Daily Nigerian cewa abokai sun hada Miliyan 10 aka bayar dan karbo sojan amma duk da haka masu garkuwar saida suka kasheshi.
Tuni dai tun a lokacin da ake maganar biyan kudin Fansa hukumar Sojin ta kaddamar da bincike dan gano sojan.