fbpx
Monday, August 8
Shadow

Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kwamishinan Nasarawa, sun nemi kudin fansa na miliyan N30

Masu garkuwa da mutane a daren Talata sun yi awon gaba da tsohon Kwamishinan Ilimi, Mai Girma Cif Clement Uhembe a gidansa da ke Lafiya.
Suna neman kudin fansa miliyan N30 domin sakin sa.
Masu garkuwan dauke da muggan makamai, sun mamaye gidan tsohon kwamishinan, wanda kuma shi ne babban malami a Sashin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Tarayya da ke Lafia da misalin karfe 8:30 na dare.
Matar shi, Mrs. Amarya Uhembe, ta fada cewa wadanda suka sace din, wadanda yawansu ya kai goma, sun mamaye gidansu inda suka kutsa kai cikin daya daga cikin gidajensu inda mijinta me kwance bayan dawowarsa daga aiki kuma suka dauke shi zuwa wani wurin da ba a sani ba.
A cewar ta: “Sun zo ne da misalin karfe 8:30 na dare suka fara kwankwasa kofa da karfi yayin da mijina ke cikin dakin. Na matsa kusa da kofar don ganin wanda yake kwankwasa sai kawai na gano cewa su mutane ne dauke da manyan makamai.
“Lokacin da na lura su mutane ne masu dauke da makamai, sai na yi sauri na rufe kofar, ina ihu don neman agaji kafin mijina ya zo ya tayani da gwagwarmayar rufe kofar, duk da cewa suna jan jiki don tilasta kansu cikin zauren.
“Mijina ya ruga zuwa kofar kuma mun yi nasarar rufe kofar amma ‘yan bindigar suka ci gaba da matsawa har sai da suka yi nasarar amfani da wasu abubuwa wajen fasa kofofin da bango don samun damar shiga.”
Ta bayyana cewa daga baya ‘yan bindigar sun ba mijinta damar yin amfani da wayarsa ta hannu don yin magana da dangin kan kudin fansa na miliyan N30.
Kokarin yin magana da hukumomin ‘yan sanda kan lamarin ya ci tura.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, PPRO, Ramhan Nansel bai iya daukar kiraye-kiraye da dama da aka mashi ba kamar yadda yake a lokacin hada wannan rahoto.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kashe insfetoci biyu tare da wani dan Indiya a wani kamfani dake jihar Imo

Leave a Reply

Your email address will not be published.