fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Masu garkuwa da mutane sun saki 4 daga cikin ma’aikatan Road Safety da suka kama

Hukumar FRSC ta bayyana cewa 4 daga cikin maaikatanta da masu garkuwa da Mutane suka sace sun kubuta bisa taimakon sauran jami’an tsaro.

 

Saidai hukumar tace har yanzu akwai sauran jami’anta 6 dake hannun masu garkuwa da mutanen. Hadimin dake kula da ilimantar da jama’a na huku3, ACM Bisi Kazeem ya bayyanawa manema labaran Kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN haka a Abuja.

Jamj’an hukumar 26 ne dake tafiya daga Kebbi zuwa Sokoto dan halartar wani horo na musamman suka gamu da harin ‘yan Bindigar inda 2 suka rasu, 10 suka bace, 8 suka tsira ba tare da wani Rauni ba sai kuma 6 suka jikkata.

Karanta wannan  Dattawan Arewa sun gargadi Atiku cewa kar ya canja Okowa a matsayin abokin takararsa

 

Shugaban hukumar, Boboye Oyeyemi ne ya nemi sauran jami’an hukumar kada gwiwarsu ta yi sanyi wajan bautawa kasa inda ya nemi da su ci gaba da jajircewa wajan aikinsu.

 

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan rayukan da suka rasa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.