Thursday, July 18
Shadow

MASU GARKUWA SUN BIDIGE MUTUM DAYA KAI MUSU KUDIN FANSAR YAN’UWAN SA NERA MILIYAN 16 DA MASHINA 3

MASU GARKUWA SUN BIDIGE MUTUM DAYA KAI MUSU KUDIN FANSAR YAN’UWAN SA NERA MILIYAN 16 DA MASHINA 3.

Daga Shuaibu Abdullahi

Rahotanni sun tabbatar da cewar matashin da aka tura ya Kai kudin fansar wasu mutane 9 da masu garkuwa suka sace, kudin da ya kai Nera miliyan 16 da babura 3 shima sun halaka shi.

City and Crime ta fitar da rahotan cewar masu garkuwa sun fara da bukatar Nera miliyan 30 bayan da suka kwashe Mutanen 9, a Unguwar Iya a Jeren Jihar Kaduna, tun ranar 16, ga watan afurelun wannan shekarar ta 2024.

Rahotan ya ce Wani makusanci ne ya tabbatar da manema Labarai cewar masu garkuwan sun daure tare da harbe Abbas, Dan kimanin shekaru 27, a lokaci guda bayan da suka karbe adadin kudaden daya Kai musu.

Karanta Wannan  Alamun ciki a watan farko

Daya daga cikin wadanda basu garkuwan suka saki, ya ce masu garkuwan sun bindige matashi Abbas, ne saboda wai lokacin da suke tattauna yarjejeniyar kudade da suke bukata a matsayin kudin fansa ya farfada musu maganganu Kuma yayi musu taurin Kai.

Zuwa yanzu jami’in Hulda da jama’a na rundunar Yan’sandan ta kasa reshen jihar Kaduna, ASP. Mansur Hassan bai ce komai ba game da batun.

To amma Shuaibu Hussain, makusanci ga Wanda aka kashe ya ce masu garkuwan sun Fadi inda aka je aka dauko gawar Abba da suka halaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *