fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Masu kula da hakkokin kananan yara a Katsina sun koka da yawaitar lalata da yara maza da mata

Majalisar dake kula da hakkokin yara a jihar Katsina ta koka da yanda ake samun yawaitar lalata da yara maza da mata.

 

Kakakin Majalisar, Ibrahim Maharazu ya bayyana rashin jin dadinsa kan lamarin a yayin ganawarsa da kungiyar, Save the Children a Daura dake jihar ta Katsina.

 

Ya bada Misalin cewa akwai wani me kudi a Daura da ya rika lalata da yara maza, yace da aka kamashi sai ya bada hakuri inda ya sha alwashin daukar nauyin yaran da ya lalata.

 

Yace Sarkin Daura ya samu labarin faruwar Lamarin har ya koreshi daga garin amma kuma daga baya sai ya koma. Yace akwai wani shima dan shekaru 23 da yawa ‘yar Shekaru 11 Fyade.

 

Kungiyar Tace kwanannan zata fitar da Matsaya akan Lamarin sannan zata rika wayarwa da mutane kai kan kare ‘ya’yansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *