fbpx
Sunday, December 4
Shadow

“Masu kushe Maulidi ku tsaya iya Iliminku: Nidai da inyi murnar zagayowar ranar haihuwata: Gara nayi ta manzon Allah(Maulidi)”>>Inji Adam A. Zango bayan da wasu suka kushe zuwan da yayi gurin Maulidi

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango da Tauraron mawaki Aminu Ala sunje wajan wani Maulidi da akayi a wata makaranta dake Rimin-kebe a cikin garin Kano inda har Adamun ya saka hotuna da bidiyon da suka dauka a gurin Maulidin shi da abokin aikin nashi a dandalinshi na sada zumunta da muhawara .


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Mutane sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi akan wannan wannan zuwan nasu gurin Maulidin, kamar dai kowane sha’ani, saidai da alama sukar da wasu sukawa Maulidin baiwa Adamu dadiba, domin kuwa ya fitar da wani gajeren bidiyo inda ya musu raddi.
Adamun dai ya bayyana cewa, ya karanta ra’ayoyin mutane akan zuwanshi gurin Maulidi kuma wasu sun yaba wasu kuwa sun kushe, amma yace ya duba wasu daga cikin wadanda suka kushe Maulidin kuma yaga suna shiga gidan daukar hoto suna daukar hotuna dan murmar zagayowar ranar haihuwarsu, ya tambaya toshin kai zakayi murnar zagayowar ranar haihuwarka amma ifan anyi ta annabi sai ka kushe?.
A karshedai Adamu ya bayyana cewa masu kushe maulidin su tsaya iya inda iliminsu yake inda ya kara da cewa shidai da yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi gara tayi ta manzon Allah, watau Maulidi.
Danjin abinda Adamun yace daga bakinshi sai a kalli bidiyonnan na sama.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  YANZU-YANZU: Gobara Ta Tashi A Dakin Kwanan Dalibai A Jami'ar Dan Fodiyo Dake Sokoto

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *