fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Masu zanga-zanga sun yi wa Ambasadan Russia wanka da jan fenti

A yau Litinin ne masu zanga-zanga a Warsaw su ka watsa wa Ambasadan Russia jan fenti, inda su ka hana shi ajiye fulawa a maƙbartar sojojin Soviet a Poland.

Kamfanin Dillacin Labarai PAP ya rawaito cewa lokacin da Ambasadan Russia ɗin,Sergey Andrejev ya isa maƙbartar ta sojojin Soviet a Warsaw, sai ƴan ƙasar Ukraine da Poland su ka tarbe shi da ihu, su na kiran sa “mai kashe mutane” “ɗan ra’ayin gurguzu”.

Ana cikin hakan ne sai a ka jefa masa jan fenti, lamarin da ya sanya Sergey Andrejev ɗin da muƙarrabansa su ka tsere zuwa cikin mota.

Duk ranar 9 ga watan Mayu rana ce a Russia da a ke bikin tunawa da nasar da Soviet ta samu a kan ƴan Nazi a Jamus a yakin duniya na ll.

Karanta wannan  'Yan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya>>Hedikwatar tsaro

Maƙabartar Soviet ɗin ta Warsaw an gina ta ne ƴan shekaru bayan an gama yakin duniya na ll, inda a ka binne sama da sojoji dubu 20 da ga 1944 zuwa 1945 a ciki.

A halin yanzu Poland ta karbi ƴan gudun hijira kusan miliyan 3.2 da ga Ukraine tun sanda Russia ta shiga ƙasar a ranar 24 ga Febrairu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.